logo

HAUSA

Manufar kasar Sin daya tak matsaya ce da daukacin kasashen duniya suka cimma

2024-08-23 21:47:55 CMG Hausa

Yau Jumma’a, yayin da take amsa tambayar manema labarai kan ko kasar Sin za ta gayyaci kasashen Afirka da aka ce wai “suka kulla huldar diplomasiya da yankin Taiwan" zuwa taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ta bayyana cewa, za a fitar da bayanai a gaba game da kasashen da za a gayyata.

Mao Ning ta jaddada cewa, manufar kasar Sin daya tak ita ce matsaya daya na daukacin kasashen duniya suka cimma, kuma kasashe guda 183 sun riga sun kulla huldar diplomassiya da Sin bisa ka'idar, kana ana fatan wasu kasashen da aka ce wai suka kulla huldar diplomassiya tare da yankin Taiwan za su gane yanayin tarihi, su gaggauta yanke shawarar da ta dace da moriyarsu.(Safiyah Ma)