An gano alamomin kamuwa da cutar karinbuwan birai a yankin Zinder da ake ci gaba da zurfafa bincike
2024-08-22 11:18:06 CMG Hausa
Cikin tsarin musanya da sanya ido kan cutukan da ke hadarin yaduwa, sakatare janar din ma’aikatar kiwon lafiya, dokta Malam Ekoye Saidou ya ba da labarin cewa an gano wasu mutane biyu da ake zaton suna dauke da alamomin cutar karinbuwan birai a cikin wata sanarwa ta ranar jiya 21 ga watan Augustan shekarar 2024.
Daga birnin Yamai abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
A cewar wannan sanarwa ta ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Nijar, wasu kasashen yammacin Afrika sun shaida bayyanar cutar karinbuwan birai ko Monkeypox, dalilin ke nan sanarwar take kiran daraktocin kiwon lafiya na yankuna da su kasance cikin shirin ko ta kwana game da wannan cuta.
A cewar ma’aikatar kiwon lafiya, a Nijar an gano wasu mutane biyu masu alamomin cutar Monkeypox ko karinbuwan birai a likitar Belbedji da ke yankin Zinder, da jami’an kiwon lafiya suke ci gaba da zurfafa bincike a dakunan gwajin samfuri.
Sakatare janar na ma’aikatar kiwon lafiya ya bukaci masu ruwa da tsaki a matakai daban daban da su karfafa sanya ido bisa dukkan bayanai da labarai na kiwon lafiya daga asibitocin gwamnati da masu zaman kansu.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.