Sin da Rasha za su fadada hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu
2024-08-22 10:43:36 CMG Hausa
Kasar Sin da Rasha za su yi aiki tare don fadada hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu, a cewar sanarwar hadin gwiwa da aka fitar jiya Laraba, bayan ganawar shugabannin kasashen Sin da Rasha karo na 29.
Firaministan kasar Sin Li Qiang da firaministan kasar Rasha Mikhail Mishustin ne suka jagoranci taron tare.
Sanarwar ta ce, bangarorin biyu sun amince da cewa, za a yi kokarin hadin gwiwa wajen kyautata tsarin cinikayya, da samar da sabbin fasahohin bunkasar tattalin arzikin da yawan cinikayya tsakanin kasashen biyu, da inganta ci gaban cinikayya ta yanar gizo.
Bangarorin biyu sun kuma amince da cewa, za a ba da goyon baya ga kasashen BRICS a hadin gwiwarsu a fannonin inganta kwarewar aiki, da bincike na hadin gwiwa, da gudanar da harkokin duniya a fannin amfani da fasashohi masu kwaikwayon tunanin dan Adam. (Mohammed Yahaya)