logo

HAUSA

Kasar Sin ta kuduri aniyar magance matsalar gine-gine ba bisa ka’ida ba don kare filayen noma

2024-08-22 16:00:12 CMG Hausa

Hukumomin kasar Sin su kuduri aniyar daukar tsauraran matakai don kiyaye filayen noma, ta hanyar bayyana kararraki da suka shafi kwacewa da rusa gine-gine.

Ma’aikatar kula da kararrakin jama’a ko SPP da ma’aikatar kula da albarkatun kasa sun wallafa wasu kararraki guda hudu daga Sichuan, Guangxi, Hebei, da Heilongjiang.

Wani jami'in SPP ya bayyana cewa, rusa gine-ginen da ba bisa ka'ida ba ya kasance kalubale ga masu gabatar da kara na kasar Sin wajen aiwatar da dokar amfani da filaye. Wannan yanayin yana bukatar bayyana gaskiyar al’amura, da bayyana hanyoyin da suka shafi aikin rusau, da kuma yadda hukumomin da abin ya shafa suke tafiyar da kararrakin yadda ya kamata. (Mohammed Yahaya)