A shirye Sin take ta hada hannu da Rasha domin karfafa hadin gwiwa a dukkan bangarori
2024-08-21 21:11:57 CMG Hausa
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya bayyana a yau Laraba cewa, a shirye Sin take ta hada hannu da Rasha domin karfafa hadin gwiwa a dukkan bangarori a tsakaninsu, da ingiza hadin gwiwarsu bisa manyan tsare-tsare a sabon zamani, zuwa wani sabon mataki.
Li Qiang ya bayyana haka ne a yau Laraba, lokacin da yake jagorantar taro karo na 29 na shugabannin gwamnatocin Sin da Rasha, tare da firaministan Rasha, Mikhail Mishustin.
A nasa bangare, Mikhail Mishustin ya ce, a shirye Rasha take ta hada hannu da Sin domin ci gaba da zurfafa aminci da juna da fadada hadin gwiwa a bangaren zuba jari da makamashi da tattalin arziki da cinikayya da al’adu da yankunansu.
Ya kuma yi alkawarin Rasha za ta hada kai da Sin wajen karfafa tuntubar juna da hadin kai game da batutuwan kasa da kasa, da kyautata kare halaltattun hakkoki da muradun bangarorin biyu da daukaka dangantakarsu bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni domin sabon zamani zuwa sabon matsayi. (Fa’iza Mustapha)