An gudanar da dandalin tattauna hadin gwiwar kafofin watsa labarai na Sin da Afirka karo na 6
2024-08-21 20:39:34 CMG Hausa
A yau Laraba, aka gudanar da dandalin tattauna hadin gwiwar kafofin watsa labarai na Sin da Afirka karo na 6 da kuma tattaunawa tsakanin cibiyoyin bincike na Sin da Afirka, a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Baki mahalarta taron sun bayyana cewa, bisa jagorantar da shugaba Xi Jinping da shugabannin Afirka suka yi bisa manyan tsare-tsare, dangantakar Sin da Afirka ta shiga sabon mataki na gina al’umma mai makomar bai daya ta Sin da Afirka tare. Sun ce taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka da za a gudanar ba da jimawa ba, zai kasance babban dandalin da zai inganta hadin kan Sin da Afirka. Kuma ya kamata cibiyoyin bincike na kafofin watsa labarai su yada ra’ayi na gaskiya da gadon zumuncin gargajiya, da kuma ba da labaran ci gaban hadin gwiwar Sin da Afirka tare, ta yadda za a ba da gudummawa da inganta zamanintar da Sin da Afirka tare.
Jigon dandalin tattaunawar shi ne “tafiya kan hanyar zamanintarwa tare”. Taron ya samu halartar wakilai fiye da 500 daga gwamnatoci da kafofin watsa labarai da cibiyoyin bincike da kuma kungiyoyin kasa da kasa na Sin da kasashen Afirka fiye da 40.(Safiyah Ma)