logo

HAUSA

Kasashen AES sun kai karar Ukraine gaban kwamitin tsaro na MDD game da goyon bayanta ga ta’addanci

2024-08-21 10:22:36 CMG Hausa

Burkina Faso, Mali da Nijar da suka hada gamayyar kasashen yankin Sahel AES, cikin wata wasikar hadin gwiwa sun kai karar Ukraine gaban kwamitin tsaro na MDD game da goyon bayan da kasar take nunawa ta’addanci a cikin wata sanarwar da kafofin yada labarai suka samu a ranar jiya Talata 20 ga watan Augustan shekarar 2024.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Ita dai wannan sanarwa ta bayyana cewa bisa umurnin shugabannin kasashen AES, muna farin cikin sanar da ku da isar da wannan wasika ta hadin gwiwa ta ranar 19 ga watan Augustan shekarar 2024, suka aika muku da sunan Karamoko Jean-Marie Traore, ministan harkokin wajen kasar Burkina Faso, Abdoulaye Diop, ministan wajen kasar Mali da Bakary Yaou Sangare ministan wajen kasar Nijar.

Ta hanyar wannan wasikar hadin gwiwa, ministocin harkokin wajen kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar sun yi tir da allawadai da goyon bayan da gwamnatin Ukraine take nunawa ta’addancin kasa da kasa, musamman ma a yankin Sahel.

Suna kira ga kwamitin tsaro na MDD da ya dauki nauyin da ya rataya kan wuyansa gaban wannan zabi karara na kasar Ukraine na taimakawa ta’addanci, ta yadda za’a yi rigakafin wadannan munanan ayyuka dake kawo barazana ga kwanciyar hankali da zaman lafiya a yankin Sahel, da ma nahiyar Afrika baki daya.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.