Za a gudanar da bikin CIFTIS na shekarar 2024 a birnin Beijing
2024-08-21 13:52:25 CMG Hausa
Za a gudanar da bikin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa na shekarar 2024 wato CIFTIS a tsakiyar watan Satumba mai zuwa a nan birnin Beijing. Bisa jadawalin aikin da aka tsara, za a bude tsarin rajistar ‘yan jarida mahalarta bikin tun daga yau Laraba 21 ga wata har zuwa Alhamis din makon gobe 29 ga watan Agustan nan.
‘Yan jarida na iya shiga shafin yanar gizo na bikin CIFTIS, wato www.ciftis.org, kana su shiga shafin halartar bikin don yin rajistar ‘yan jarida. (Zainab Zhang)