Kasar Sin: Shirin EU na kakaba haraji kan motoci masu amfani da lantarki na kasar Sin ya sabawa tarihi
2024-08-21 19:55:50 CMG Hausa
A martaninta game da shirin kungiyar Tarayyar Turai EU na kakaba haraji mai yawa kan motoci masu amfani da lantarki kirar kasar Sin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Mao Ning, ta bayyana yayin taron manema labarai na yau cewa, binciken wata dabara ce ta kariyar cinikayya da babakere, da watsi da gaskiya da ma ka’idojin hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO, lamarin da ya sabawa tarihi da lalata shirin EU na komawa ga amfani da makamashi mai tsafta da ma kokarin da duniya ke yi na yaki da sauyin yanayi. Bugu da kari, ta ce matakin zai yi wa wasu illa da ma ita kanta Turai. (Fa’iza Mustapha)