logo

HAUSA

DGPC na Nijar: Sabon sakamakon ambaliyar ruwa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 131 da raunata 133

2024-08-21 10:19:31 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, a cikin rahotonta da take fitarwa mako-mako, ma’aikatar da ke kula da kare fararen hulla ta DGPC ta fitar da wani sabon rahoto a ranar jiya Talata 20 ga watan Augustan shekarar 2024 a birnin Yamai da ya shafi kasar baki daya.

Daga birnin Yamai din abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Wannan sabon rahoto ya nuna cewa, ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 131, yayin da mutane 133 suka ji rauni, kana fiye da iyalai 31,963 suka tsintsi kansu cikin wannan matsala zuwa ranar 14 ga watan Augustan shekarar 2024, a cewar ma’aikatar dake kula da kare fararen hulla ta DGPC.

A cewar ma’aikatar DGPC, yankin Maradi shi ne yanki mafi shafa da ambaliyar ruwa tare da mutuwar mutane 16 ta hanyar nutsewa cikin ruwa yayin da mutane 31 ta hanyar rugujewar gidaje, sannan yankin Tahoua tare da mutuwar mutane 15 ta hanyar nutsewa cikin ruwa, kana mutane 13 ta hanyar faduwar gidaje, sannan na uku yankin Zinder da ya samu mutuwar mutum 7 ta hanyar nutsewa cikin ruwa kana mutane 21 ta hanyar faduwar gidaje.

Baya ga wannan, mutane 245,098 matsalar ta shafa, gidaje 26,914 suka fadi, kana dabobbi fiye da 16,505 aka rasa.

A cewar ma’aikatar dake kula da kare al’umma, wadannan ambaliyar ruwa sun shafi jihohi 49, kananan hukumomi 146 da kuma kauyuka tare da unguwanni 1,015.

Mamane ada, sashen Hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar