DRC za ta karbi kason alluran rigakafin cutar kyandar biri a mako mai zuwa
2024-08-20 14:07:51 CMG Hausa
Ministan ma’aikatar lafiya na Jamhuriyar dimokaradiyyar Congo ko DRC Roger Kamba, ya ce kasarsa za ta karbi wani kaso na alluran rigakafin cutar kyandar biri a mako mai zuwa, bayan da aka ayyana cutar a matsayin barazanar lafiyar al'umma dake bukatar daukin gaggawa a duniya.
Kamba, wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin, ya ce tun bayan barkewar cutar a farkon shekarar nan, an tattara alkaluman mutane 16,700, da ko dai an tabbatar, ko kuma ana zaton sun harbu da cutar, ciki har da mutane 570 da ta hallaka. Kaza lika, adadin da aka tattara a makon nan ya karu daga mutane 15,664 da aka yi zargin sun harbu, da mutane 548 da suka rasu sakamakon cutar a makon jiya.
A watan Disamban shekarar 2022, Jamhuriyar dimokaradiyyar Congo ta ayyana barkewar cutar kyandar biri, lamarin da ya wajabta kafa tsarin gaggawa na lura da yaduwarta tun daga watan Fabarairun 2023, bisa karuwar alkaluman masu harbuwa da ita.
Da yake tsokaci game da matakan da gwamnati ke dauka, mista Kamba ya ce yin alluran rigakafi, daya ne kawai daga matakan shawo kan annobar, domin kuwa matakin farko shi ne kandagarkin bullarta. Ya ce matakan da gwamnati ta riga ta dauka sun taimaka matuka wajen dakile fadadar bazuwar cutar a cikin kasar. (Saminu Alhassan)