logo

HAUSA

Xi ya gana da shugabannin majalisun dokokin kasashen duniya

2024-08-20 21:13:13 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da yammacin yau Talata a nan birnin Beijing, da shugabannin majalisun dokoki na kasashen duniya dake halartar bikin cika shekaru 40 da shigar majalisar wakilan jama’ar kasar Sin cikin kungiyar majalisun dokoki da kuma taro karo na 6 na mambobin majalisun dokokin kasashe masu tasowa.

Xi Jinping ya ce, kasar Sin ba ta neman zamanantar da kanta ita kadai, kuma a shirye take ta hada hannu da sauran kasashe masu tasowa da sauran kasashen duniya wajen inganta zamanantar da duniya da zai kunshi samar da ci gaba cikin lumana da hadin gwiwar moriyar juna da wadata na bai daya da hada hannu domin zama karfi mai tabbatar da zaman lafiya a duniya kuma kashin bayan ci gaba ba tare da rufa-rufa ba da jagorantar harkokin duniya da kuma karfin ingiza koyi da juna tsakanin mabambantan al’ummu. (Fa’iza Mustapha)