A shirye Sin take ta hada hannu da dukkan bangarori wajen ba da gudummuwa ga kyautata tsarin cinikin makamai a duniya
2024-08-20 19:53:00 CMG Hausa
Yayin da ake cika shekaru 10 da fara aiki da yarjejeniyar cinikin makamai ta duniya ATT, kasar Sin ta tura tawagarta zuwa taro karo na 10 na kasashen da suka rattaba wa yarjejeniyar hannu, wanda ke gudana a Geneva na Switzerland.
Don gane da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta ce cikar yarjejeniyar shekaru 10, wani sabon mafari ne. Tana mai cewa, a shirye Sin take ta hada hannu da dukkan bangarori wajen bayar da gudummuwar basirarta ga inganta jagorantar harkokin da suka shafi yarjejeniyar makamai ta duniya da samar da daidaito da tabbaci ga duniya mai cike da rashin tabbas.
Ta ce, kasar Sin ta kasance mai goyon baya kuma mai aiwatar da yarjejeniyar ta ATT. Kuma tana nuna sanin ya kamata don gane da batun da ya shafi cinikin makamai da sauran ayyuka masu ruwa da tsaki domin cimma tanadin yarjejniyar. Bugu da kari, ta ce Sin tana hadin gwiwa ne da cinikin makamai da kasashen dake da cikakken ‘yancin kai, kuma ba ta sayar da su ga wadanda ba kasashe ba ne. (Fa’iza Mustpha)