logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya gana da firaministan kasar Fiji

2024-08-20 21:28:03 CMG Hausa

Da yammacin yau Talata 20 ga wata ne, shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya gana da firaministan kasar Fiji, Sitiveni Rabuka, wanda a yanzu haka ke ziyarar aiki a kasar Sin, a babban dakin taron al’umma dake birnin Beijing.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, Fiji, ita ce kasa tsibiri na farko dake yankin tekun Pasifik, wadda ta kulla huldar diflomasiyya da kasar Sin, kana a shekara mai kamawa, za a cika shekaru 50 da kulla wannan hulda tsakanin kasashen biyu. Tun kusan rabin karnin da ya gabata, har zuwa yanzu, kasashen biyu na mara wa juna baya, da taimakawa juna, al’amarin da ya sa suka zama tamkar abun koyi ga shimfida adalci da sada zumunta da hadin-gwiwa tsakanin babbar kasa da karama. Kasar Sin ta bayyana fatan yin kokari tare da Fiji, don raya al’ummomin kasashen biyu masu kyakkyawar makoma ta bai daya, don kara samar da alfanu ga al’ummominsu baki daya.

Shi ma a nasa bangaren, Rabuka ya ce, ya taba ziyartar kasar Sin shekaru 30 da suka wuce, a matsayinsa na firaministan kasar Fiji a wancan lokaci, kuma ya taba ziyartar lardunan Yunnan da Fujian da Zhejiang da sauransu, inda ya gane ma idanunsa manyan nasarori da abubuwa masu ban al’ajabi da suka wakana a kasar Sin a karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, a fannonin da suka jibanci rage talauci da samar da ci gaba, al’amuran da suka burge shi matuka.

Rabuka yana mai fatan koyon muhimman dabaru da hikimomin kasar Sin, da inganta hadin-gwiwa da kasar, a fannonin rage talauci, da gina muhimman ababen more rayuwar al’umma, da kara tuntubar juna da sauransu. Kaza lika, firaministan ya ce kasarsa na fahimtar matsayin gwamnatin kasar Sin kan batun Taiwan dari bisa dari, kuma za ta ci gaba da tsayawa kan manufar Sin daya tak ce a duniya. (Murtala Zhang)