Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta fara cinikin hajar danyen mai ta amfani da kudin Naira daga 1 ga watan Oktoba
2024-08-20 11:07:09 CMG Hausa
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da cewa za a fara biyanta da kudin Naira daga cinikin dayen man da za ta fara sayarwa matatar Dangote da sauran kamfanonin tace mai na cikin gida daga ranar 1 ga wata Oktoban bana.
Ministan kudi da raya tattalin arziki Mr Wale Edun ne ya tabbatar da hakan a Abuja ranar Litinin 19 ga wata yayin taron farko na kwamatin aiwatar da tsarin cinikin danyen mai ta amfani da takardun naira, ya ce fara wannan hada-hada zai kai ga Najeriya zuwa ga wani mahimmin matsayi a sauye-sauyenta na tattalin arziki.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Ministan kudin na tarayyar Najeriya haka kuma ya ce ana sa ran a cikin watan gobe na satumba, tataccen man fetur na farko daga matatar man Dangote zai shigo kasuwa kamar yadda yake kunshe a yarjejeniyar da aka kulla.
Mr Wale Edun ya bayyana taron ‘yan kwamiti a matsayin daya daga cikin mahimman matakan aiwatar da umarnin shugaban kasa wanda ke da nufin bukasa tattalin arzikin kasa.
Ministan ya ce a yayin zaman kwamatin an yi duba a kan wasu daga cikin nasarorin da aka samu kama daga fara cinikin danyen man da kudin Naira ga matatar man Dangote da sauran matatu, sannan kuma an tattauna a kan hanyoyin da za a samu nasarar wannan hada hada a karon farko a tarihi.
Har ila yau ministan ya yi albishir da cewa daga watan Nuwanban 2024 Najeriya za ta samu wadatuwar man fetur a cikin gida saboda samuwar man matatar Dangote da matatar man Fatakwal wadda aka farfado da aikinta.