Amurka ba ta da hakkin tsoma baki cikin batutuwan teku dake tsakanin Sin da Philippines
2024-08-20 20:11:49 CMG Hausa
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, Amurka, a matsayinta na wadda ba ta da ruwa da tsaki a batun tekun kudancin kasar Sin, ba ta da hakkin shiga tsakani kan batutuwan teku dake tsakanin Sin da Philippines.
Kakakin ma’aikatar Mao Ning ce ta bayyana haka yayin taron manema labarai na yau, lokacin da take mayar da martani don gane da tambayar da aka yi mata game da sukar da Amurka ta yi wa matakan da Sin ta dauka a tekun kudancin kasar, biyo bayan kutsen da jiragen ruwa biyu na Philippines suka yi a yankin ruwan dake kusa da sashen tudun ruwa na Xianbin Jiao na tsibiran Nansha Qundao a ranar Litinin.
Mao Ning ta jaddada cewa, Philippines ce ta fara take hakkokin kasar Sin, inda Sin ta dauki matakai bisa doka na kare ‘yancinta da hakkoki da muradu, wadanda suka dace da doka kuma bai kamata a ga baikenta ba.
Ta ce Amurka, ba ta da ruwa da tsaki cikin batun, kuma ba ta da wani hakki na shiga tsakani, kana bai kamata ta yi amfani da yarjejeniyar tsaro dake tsakaninta da Philippines a matsayin wadda za ta fake da ita domin keta ‘yanci da hakkokin Sin a tekun kudancin Sin ba. (Fa’iza Mustapha)