logo

HAUSA

Xi ya yabawa ‘yan wasan Olympics na Sin da suka samarwa kasar daukaka

2024-08-20 20:19:21 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yabawa ‘yan wasan Olympics na kasar saboda kwazo da rawar da suka taka a gasar wasannin Olympics ta Paris, yana mai cewa, nasarar da suka samu ta samar da daukaka ga kasar.

Da yake ganawa da tawagar Sin da ta halarci gasar wasannin Olympics ta Paris ta shekarar 2024, yau Talata a babban dakin taron jama’a, shugaba Xi ya bukaci su kara kokarin gina kasar Sin domin ta zama mai karfi a fagen wasanni. (Fa’iza Mustapha)