logo

HAUSA

Kasar Sin ta lashi takobin dakile duk wani yunkurin keta doka bayan kutsen Philippine a tekun kudancin kasar

2024-08-19 20:31:27 CMG Hausa

Rundunar tsaron teku ta kasar Sin CCG, ta lashi takobin dakile duk wani yunkurin keta doka da takala, tare da kare ikon kasar kan yankunanta da ma hakkoki da muradunta na teku, biyo bayan kutse na baya-bayan nan da Philippine ta yi a tekun kudancin Sin.

Da take tsokaci kan lamarin a yau Litinin, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta ce, alhakin karo da jiragen ruwan kasashen biyu suka yi na kan Philippine, kuma Sin za ta ci gaba da daukar tsauraran matakai masu karfi, wadanda suka dace da doka wajen kare ikonta kan yankunanta da hakkoki da muradunta na teku tare da kiyaye yarjejeniyarsu don gane da tekun.

Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta kuma bukaci Philippine ta kiyaye yarjejeniyar wucin gadi da ta cimma da Sin, ta kauracewa aiwatar da abubuwan da ka iya rikita lamarin da kuma hada hannu da Sin wajen tafiyar da batun yadda ya kamata. (Fa’iza Mustapha)