logo

HAUSA

Kwamitocin Sin da Amurka kan harkokin kudi sun gudanar da taro karo na 5

2024-08-19 20:13:51 CMG Hausa

Kwamitocin kasashen Sin da Amurka kan harkokin kudi sun gudanar da taro karo na 5 a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin, daga ranar Alhamis zuwa Juma’a, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi manufofin kudi na kasashen biyu.

Mataimakin gwamnan babban bankin kasar Sin Xuan Changneng da Brent Neiman, mataimakin sakataren kula da harkokin kudi na kasashen waje a Baitul-malin Amurka ne suka jagoranci taron.

Bangarorin biyu sun yi tattaunawa cike da kwarewa da gaskiya da ma’ana kan manufofin kudi da ke jan hankalinsu, ciki har da manufar kara zurfafa cikakken gyare-gyare, kamar yadda aka tattauna a zama na 3 na kwamitin tsakiya na JKS karo na 20.

Tattaunawar ta kuma tabo batutuwa kamar na yanayin tattalin arziki da hada-hadar kudi da manufofin kudi da hannayen jari da kasuwarsu da biyan kudi da bayanai tsakanin kasa da kasa da jagorantar harkokin kudi na kasa da kasa da fasahohin kudi da samar da kudi ga ayyuka masu dacewa da kare muhalli da yaki da halasta kudin haram da samar da kudi ga ayyukan ta’addanci. (Fa’iza Mustapha)