An rufe taron kolin kunigyar SADC
2024-08-19 11:30:09 CMG Hausa
A Jiya Lahadi, an rufe taron kolin kungiyar raya kudancin Afirka wato SADC karo na 44 a birnin Harare, fadar mulkin kasar Zimbabwe. Babban taken taro na wannan karo shi ne, “neman dauwamammen ci gaban tattalin arziki ta hanyar yin kirkire-kirkire, tare da inganta harkokin masana’antu na mambobin kungiyar SADC”.
A yayin taron, shugabannin sun nuna damuwarsu game da hare-haren da aka kai ga Falesdinawa, inda suka yi kira da a tsagaita bude wuta nan take, da kuma sakin mutanen da aka tsare. An kuma jaddada aniyar soke takunkumin da yammacin kasashen duniya suka kakkaba wa kasar Zimbabwe, gami da yin tattaunawa kan yanayin yaduwar annobar cutar kyandar biri a nahiyar Afirka. Haka zalika, shugabannin sun yi tattaunawa kan aikin shimfida zaman lafiya da yanayin tsaro a kasashen Mozambique da Congo Kinshasa. (Maryam Yang)