logo

HAUSA

Hukumar yaki da yaduwar cutuka ta kasa a Najeriya ta ce an samu rahoton bullar cutar kyadar biri 39 a kasar

2024-08-17 10:39:10 CMG Hausa

Hukumar yaki da yaduwar cututtuka a tarayyar Najeriya ta ce, ya zuwa yanzu ta samu rahoton bullar cutar kyandar biri har 39 a jahohi 33, ciki har da Abuja.

Darkata janaral na hukumar Mr Jide Idris ne ya tabbatar da hakan a birnin Abuja a kwanan baya, lokacin da yake yi wa manema labarai bayani a game da cutar da kuma bukatar daukar matakan gaggawa na kare al`umma daga kamuwa da ita .

Daga tarayyar Najeriya wkailin mu Garba Abdullahi bagwai ya aiko mana da rahoto.

Mr Jide Idris ya ce a halin yanzu hukumar ta kara tsananta sanya idanu domin ganowa da kuma gaggauta kai dauki ga wadanda aka samu rahoton sun kamu da ita wannan cuta.

Kamar yadda ya fada jami`an hukumar na aikin hadin gwiwa da sauran cibiyoyin kiwon lafiya a tasoshin jiragen ruwa guda 10 da kan iyakoki 51 dake Najeriya domin dai yin kandagarkin yaduwar cutar.

Haka kuma shugaban hukumar dakile cuttutuka masu yaduwa ta kasa ya ce hukumar tasu ta sanya ido sosai a kan wasu jahohin kasar, da suka hada da Legos, Enugu, Kano,Rivers, Cross-rivers, Akwa Ibom, Adamawa ,Taraba da babban birnin tarayya Abuja,domin tabbatar da ganin  cutar kyandar birin batayi ta`adi ba kamar yadda ake hasashe. (Garba Abdullahi Bagwai)