Sin ta samu ci gaba a fannin raya jarin fasahohin kere-kere da kaso 10.9% a watanni 7 na farkon bana
2024-08-17 16:21:18 CMG Hausa
Tun daga farkon shekarar nan ta 2024, kasar Sin ta aiwatar da jerin sabbin matakai, ciki har da na tallafawa manufofin hada hadar kudi, da daga matsayin sashen fasahohin kere-kere da kayayyakin aiki, da nufin ingiza nasarar kasuwannin cikin gida, da ingiza samar da ci gaba maras gurbata muhalli, da fitar da mafi karancin iskar carbon mai dumama yanayi.
Alkaluman baya bayan nan sun nuna yadda ta karkashin manufofin sabunta kayayyakin aiki masu tarin yawa, Sin ta samu gagarumin ci gaba, a fannin raya jarin fasahohin kere-kere, wanda ya bunkasa da kaso 10.9 bisa dari a watanni 7 na farkon shekarar bana.
Kari kan hakan, yadda masana’antun Sin ke samun karin kyautatuwar amfani da makamashi yana fadada, kana adadin makamashi da ake amfani da shi a kasar kan duk ma’aunin GDP na kara raguwa, yayin da kasar ke kara zaburar da ci gaba ta hanyoyin da ba sa gurbata muhalli, da masu fitar da mafi karancin iskar carbon. (Saminu Alhassan)