Najeriya da kasar Equatorial Guinea sun sanya hannu kan yarjejeniyar shimfida bututun iskar gas a yankin gabar kogin Guinea
2024-08-16 09:12:21 CMG Hausa
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tnubu da takwaransa na kasar Equatorial Guinea Teodoro Mbasogo sun sanya hannu a kan yarjejeniyar aikin shimfida bututun gas a yankin gabar kogin Guinea, haka kuma yarjejeniyar ta kunshi kara jaddada ayyukan hadin gwiwa da za su ciyar da kasashen gaba.
Shugabannin biyu sun sanya hannun kan yarjejeniyar ce a ranar Laraba 14 ga wata a Malabo, babban birnin kasar ta Equatorial Guinea.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Kamar dai yadda yake kunshe cikin wata sanarwa dauke da sanya hannun mai magana da yawun shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Mr Ajuri Ngelale wanda kuma aka rabawa manema labarai a birnin Abuja, yarjejeniyar ha ila yau ta hada da samar da dokoki da matakan da za a bi wajen shimfida bututun, sauran kuma sun hada da yadda za a ci gajiyar aikin da wuraren da aikin zai rinka yada zango da kuma tsarin mallakar kadarar.
A jawabinsa yayin sanya hannun, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce, yarjejeniyar za ta bude wasu sabbin damarmakin samar da gas da kuma na aiyukan yi.
Shugaban na tarayyar Najeriya ya ce, sun kuma tattauna da takwaran nasa na Guinea a kan batutuwan da suka shafi samar da aikin yi, da samar da abinci da warware matsalolin tashe-tashen hankula a nahiyar Afrika.
A nasa jawabin shugaban kasar ta Equatorial Guinea, cewa ya yi akwai dadaddiyar dangantaka tsakanin Najeriya da kasarsa, kuma za su yi amfani da wannan alaka wajen ingiza batun burin kasashen Afrika na samun mazaunin din-din-din a kwamatin tsaro na majalissar dinkin duniya, wanda hakan zai kawo ci gaban nahiyar mutuka. (Garba Abdullahi Bagwai)