logo

HAUSA

An kaddamar da kwamitin da zai samar da matakan da za a bi wajen sayar da danyen mai ta amfani da kudin Naira a Najeriya

2024-08-16 09:13:23 CMG Hausa

Ministan kudi na taryyar Najeriya Mr Wale Edun ya kaddamar da kwamitin aiwatar da tsare-tsaren sayar da danyen mai ga kananan matatun mai na cikin gida da kuma katafaren matatar man Dangote ta amfani da kudin Naira.

Ministan ya kaddamar da ’yan kwamitin ne ranar Alhamis 15 ga wata a birnin Abuja. Ya ce, an zartar da hakan ne bisa umarnin da shugaban kasa ya bayar wanda ke da nufin kara habaka sha’anin tace mai a cikin gida domin bunkasa harkokin tattalin arziki.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Ministan kudin na tarayyar Najeriya ya ce, wannan mataki da gwamnati ta dauka na fara cinikin danyen mai da kudin Naira ga matatun cikin gida, zai kawo karshen matsaloli da irin wadannan matatu ke fuskanta wajen neman dala da za su yi odar man daga waje, kari kuma da rashin tabbas na daidaitaccen farashin kudaden musaya.

Ministan ya ce, babban aikin ’yan kwamitin shi ne fitar da jadawalin da zai tafiyar da tsarin cikin nasara, domin tabbatar da ganin cewa Najeriya ta bunkasa kan sha’anin tace man fetur da kuma karfafa gwiwar kwararru na cikin gida a bangaren makamashi.

’Yan kwamitin dai sun kunshi babban sakatare a ma’aikatar kudi ta tarayya, da shugaban hukumar tara kudaden haraji na kasa, sai kuma wakilai daga kamfanin mai na kasa wato NNPC, da babban bankin Najeriya CBN da wakilai na wasu bankuna. (Garba Abdullahi Bagwai)