Ma’aikatar tsaron gidan kasar Sin: Amurka na yunkurin nuna fin karfinta bisa amfani da makamashin nukiliya
2024-08-16 20:26:11 CMG Hausa
Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron gida ta kasar Sin, Zhang Xiaogang, ya yi bayani kan batutuwan da suka shafi aikin soja a yau Jumma’a 16 ga wata.
Kakakin ya ce, Amurka, kasa ce dake kawo barazanar makamashin nukiliya mafi girma a duniya. Ita ce kuma ke bin manufar amfani da makaman nukiliya tun farkon farawa, wadda ta zuba makudan kudade a ’yan shekarun nan, a wani yunkuri na amfani da makaman nukiliya a zahirance, da kara tallata makaman nukiliya ta hanyar da ba ta dace ba, tare kuma da nuna fin karfinta, da tsorata duniya bisa makamashin nukiliya, wanda hakan ya bayyana a fili.
Kaza lika, game da matakan soja da kasashen Amurka da Japan suka dauka, wadanda suka jibanci tekun kudancin kasar Sin, kakakin ya ce, kasashe kamar su Amurka da Japan da ba sa wannan yankin, suna yunkurin hura wutar rikici babu tsayawa, sai dai ita kasar Philippines, tana son bin umarninsu, wanda hakan abun kunya ne.
Kakakin ya kara da cewa, kasar Philippines ta hada baki da kasashen da ba sa yankin, inda suka gudanar da sintirin jiragen ruwa cikin hadin-gwiwa a yankin tekun kudancin kasar Sin, al’amarin da ya saba wa sanarwa kan matakan bangarori daban-daban na tekun kudancin kasar Sin, kuma hakan sam ba zai samu goyon-baya ba, duk da yunkurin da aka yi na rufe sirrin hakan. (Murtala Zhang)