logo

HAUSA

Rundunar sojin Nijeriya ta kashe mutane 147 da ake zargin ’yan bindiga ne a makon da ya gabata

2024-08-16 11:14:34 CMG Hausa

Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cewa, cikin makon da ya gabata, dakarunta sun kashe sama da mutane 147 da ake zargin ’yan bindiga ne a wurare daban-daban yayin ayyukansu na dakile bata gari a fadin kasar.

Kakakin rundunar Edward Buba, ya shaidawa manema labarai jiya a Abuja, babban birnin kasar, an kuma cafke a kalla wasu 381 yayin ayyukan, inda rundunar ta kara matsa kaimi a yunkurinta na dakile bata gari a kasar.

A cewarsa, dakarun sun kuma yi nasarar ceto mutane a kalla 113 da aka sace, yayin da suka kwato makamai daban-daban sama da guda 74 da alburusai 3,498. (Fa’iza Mustapha)