Ruwan masu karfi sun hadasa mutuwar a kalla mutane 52 a Tillia da ke cikin yankin Tahoua
2024-08-15 18:30:52 CMG Hausa
A jamhuriyyar Nijar, ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka samu a ranakun 12 da 14 ga watan Augustan shekarar 2024 a jahar Tillia dake yankin Tahoua sun sanadiyyar mutuwar mutane 52 a yayin da ruwa suka tafi da motoci biyu.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da rahoto.
Su dai wadannan motoci na jigilar fasinja sun fito daga birnin Tahoua shake da mutane da kayayyaki, bayan an kare cin kasuwar garin Telemces da ke ci mako-mako, sun nutse cikin ruwan korama ta Garin Ali mai tazarar kilomita 70 daga arewacin Tahoua, a cewar kamfanin dillancin labarai na kasa ANP da ya rawaito kalaman hukumomin wurin, a ranar jiya 14 ga watan Augustan.
Ruwan korama sun wani matsayin cika, tare da malalar ruwan tafkuna. Wannan hadari ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 52 yayin da wasu da dama suka ji rauni a cewar majiyoyin wurin.
A halin yanzu, ’yan kwana-kwana tare da mutanen gari sun ci gaba da neman sauran gawawwaki, duk da matsalolin da ake fuskanta ganin yanayin damina yake a wannan lokaci, in ji shugaban ’yan kwana-kwanan wurin.
A yayin da jami’an tsaro na FDS, musamman jandarma da garde nationale suke ba da tsaro da kai agaji.
Yawancin ’yan kasuwa da suka rasa rayukansu na birnin Tahoua ne, da kuma wasu ’yan asilin Nijeriya. (Mamane Ada)