Jiragen ruwan tsaron teku na Sin sun fatattaki jiragen Japan da suka shiga yankin kasar Sin bisa take doka
2024-08-15 13:58:32 CMG Hausa
Kwale-kwalen kamun kifi na Tsurumaru ya shiga yankin ruwan kasar Sin na tsibiran Diaoyu ba bisa ka’ida ba a jiya Laraba, inda jiragen ruwan tsaron teku na kasar Sin suka dauki matakan da suka dace da doka tare da yi masa gargadin fita daga yankin. Tsibirin Diaoyu da sauran tsibiran dake karkashinsa, yankuna ne mallakar kasar Sin. Don haka, kasar Sin ta bukaci Japan ta dakatar da ayyukanta da suka sabawa doka nan take. Bugu da kari, jiragen ruwan kasar Sin za su ci gaba da ayyukan tabbatar da doka da kare hakkokin Sin na ruwa domin kare cikakken ’yanci da tsaro da muradu da hakkokinta. (Fa’iza Mustapha)