Taron magabata da ya kunshi gwamnoni da tsoffin shugabannin Najeriya ya jaddada goyon bayansa ga shugaba Tinubu
2024-08-14 09:59:38 CMG Hausa
Taron magabata da ya kunshi gwamnoni da tsoffin shugabannin Najeriya ya gabatar da goyon bayansa ga manufofi da tsare-tsaren gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Mahalarta taron sun tabbatar da hakan ne a taron da suka gudanar a fadar shugaban kasa dake birnin Abuja jiya Talata 13, sun ce shugaban na Najeriya ya cancanci yabo da kara samun goyon baya bisa la’akari da matakan farfado da tattalin arziki da zaman lafiya da ya bijiro da su.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
A lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron wanda ya sami halartar tsoffin shugabannin Najeriya guda biyu Dr Goodluck Ebele Jonathan da Muhammadu Buhari. Ministan ma’adanai na tarayyar Najeriya Mr. Dele Alake ya ce, an tattauna a kan yanayin tsaron kasa musamman batun zanga-zangar gama gari da aka gudanar kwanan nan, inda mashawarcin shugaban kasa kan al’amuran tsaro Malam Nuhu Ribadu ya yi bayani daki da daki.
Mininstan ya ce, dukkan bakin wadanda suka halarci taron ya zo daya, inda suka bayyana cewa babu yadda za a yi a kyale wasu mutane su yi kokarin kawo cikas ga tsarin dimokuradiyya a kasa. Sun ce zanga-zanga ba ita ce hanyar kawo sauyin shugabanci ba, inda suka kara da cewa, sauyi yana zuwa ne kawai ta hanyar kada kuri’a yayin zabe.
Tsoffin shugabannin Najeriya guda biyu Janaral Abdulsalami Abubakar da Janaral Yakubu Gawon sun halarci taron ne ta hanyar kafar intanet. (Garba Abdullahi Bagwai)