An bude dandalin raya matasa na duniya a birnin Beijing
2024-08-13 10:59:10 CMG Hausa
A jiya Litinin ne aka bude dandalin raya matasa na duniya na shekarar 2024 a nan birnin Beijing, inda sama da matasa 2,000 daga kasashe sama da 130 da kungiyoyin kasa da kasa 20 suka halarci wurin taron da kuma ta yanar gizo.
Ranar Litinin ce ranar matasa ta duniya. A cikin wani sakon bidiyo, mataimakiyar Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed ta ce, matasa su ne ginshikin ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD ta 2030 tare da yin kira da a kara ba da taimako ga ci gaban matasa.
Amina Mohammed ta ce dole ne gwamnatoci, kungiyoyi masu zaman kansu, kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin farar hula su samar da albarkatu da dandalin da matasa ke bukata don bayyana ra'ayoyinsu, yayin da ta kuma sha alwashin cewa ofishin matasa na MDD zai hada kai da tsarin MDD da kungiyoyin da suka dace a duniya don kara kaimi ga muryoyin matasa.
Matasa mahalarta taron za su kuma yi rangadi a wasu biranen kasar Sin kamar su Nanning da Hangzhou a cikin kwanaki masu zuwa, da kuma yin shawarwari kan samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli, da bunkasa fasahar zamani, da al'adun gargajiya da kirkire-kirkire, da kuma biranen da za su sa kaimi ga ci gaban matasa.
Mashirya dandalin sun ce, taron mai taken "Samun kyakkyawar makoma tare", ana sa ran zai zama muhimmin lokaci na hada karfi da karfe don aiwatar da ajandar MDD na 2030 don ci gaba mai dorewa da kuma shirin ci gaban duniya baki daya.
Kungiyar matasan kasar Sin baki daya, MDD dake kasar Sin, da kwamitin shirya dandalin ne suka dauki nauyin taron. A shekara ta 2022 ne aka gudanar da dandalin na farko. (Mohamed Yahaya)