logo

HAUSA

Firaministan kasar Nijar Ali Mahamane Lamine na ziyarar aiki a kasar Aljeriya

2024-08-12 09:46:35 CMG Hausa

 

Firaministan kasar Nijar kuma ministan kudin Ali Mahamane Lamine Zeine tare da rakiyar wata babbar tawaga ya bar birnin Yamai a ranar jiya Lahadi 11 ga watan Augustan shekarar 2024 da yamma domin wata ziyarar aiki a hukumance a kasar Aljeriya.

Daga birnin Yamai, abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Ita dai wannan ziyara ta Ali Mahamane Lamine Zeine a kasar Aljeriya ta biyo bayan wanda ta kai a kasar Morocco a ranar 12 ga watan Febrairun shekarar 2024.

Wannan ziyara na zuwa daidai da lokacin da kasashen suke kokarin kara karfafa dangantaka, musamman ma kan muhimman bangarori biyu da suka hada tsaro da makamashi.

Kasashen Nijar da Aljeriya na son kawo wani sabon lumfashi ga ci gaban huldar dangantakarsu, tare da burin karfafa zumunci da abokantaka tsakaninsu.

A bayaninsa na farko gaban ’yan jarida, firaministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine ya furta cewa wannan ziyara a kasar Aljeriya na da manufofi guda biyu zuwa uku, na farko duba hanyoyin magance matsalar tsaro tare da hada karfi da karfe wajen dakile ta’addanci a kan iyakokin kasashen biyu, sannan kuma da karfafa huldar kasuwanci da makamashi.

Mamane Ada, sashen Hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyar Nijar.