logo

HAUSA

Hukumar tsaro ta Civil Depense a Najeriya ta tura jami’anta dubu 10 domin kare manoma daga harin ’yan ta’adda a jihohin arewacin kasar

2024-08-12 09:39:14 CMG Hausa

 

Hukumar tsaron fararen hula ta Civil Depence a tarayyar Najeriya ta tura dakarunta har dubu goma zuwa jihohin arewacin kasar 19 ciki har da Abuja domin kare gonaki da kuma manoma daga farmakin ’yan ta’adda.

Babban jami’in yada labarai na hukumar Mr Babawale Afolabi ne ya tabbatar da hakan a karshen makon jiya lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Abuja. Ya ce an dauki wannan mataki ne a kokarin da ake yi na wadata kasa da abinci.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. ///

 

Hukumar tsaron ta Civil Depence ta ce ya zama wajibi a dauki matakin kare gonakin kasar da kuma manoman da suke aiki a cikin gonakin saboda hare-haren ta’addancin da ake samu a wasu sassan kasar, wanda yana matukar shafar sha’anin samar da abinci a Najeriya.

Jami’in yada labaran hukumar ya ce, daga cikin aikin wadannan dakaru ya hadar da daidaita rikici dake faruwa tsakanin manoma da makiyaya da kuma kare kayan amfani da aka shuka da kuma lafiyar manoman.

Mr. Babawale Afolabi ya ci gaba da cewa, hukumar tsaron ta Civil Depence ta zartar da shawarar tura jami’an nata ne bisa hadin gwiwa da ma’aikatar gona ta tarayya da kuma kungiyoyin kasa da kasa, inda ya sanar da cewa a tsakanin watan Janairu zuwa Maris na wannan shekara manoma 165 ’yan bindiga suka hallaka a gonakinsu, lamarin da ya zama babban kalubalen da ya kamaci daukar mataki a kai.

Ya ce, dakarun suna cikkaken kwarewa a kan yadda za su gudanar da aikin, kuma akwai kyakkyawan fatan cewar za a cimma nasarar da ake nema. (Garba Abdullahi Bagwai)