Kasar Sin ta yi kira da kar rura wutar yaki yayin da sojojin Ukraine suka shiga Kursk na Rasha
2024-08-12 14:47:28 CMG Hausa
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin a yau Litinin ta yi kira da a sassauta rikicin Rasha da Ukraine bayan rahotannin baya-bayan nan na cewa sojojin Ukraine sun shiga yankin Kursk dake kan iyakar Rasha.
A cikin wata sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce, kasar Sin za ta ci gaba da tuntubar al’ummar kasa da kasa, da taka rawar da ta dace wajen sa kaimi ga warware rikicin ta hanyar siyasa.
Ta kara da cewa, kasar Sin tana kira ga dukkan bangarorin da su mutunta "ka'idoji guda uku" na sassauta rikicin wato kar a fadada fagen daga, kar a tsananta yakin, kuma kar a rura wutar yakin daga kowane bangare. (Mohamed Yahaya)