Rayuwar halittun ruwa na kara kyautata a Kogin Yangtze
2024-08-12 20:27:02 CMG Hausa
Wata sanarwar hadin gwiwa ta ma’aikatar noma da kauyuka ta kasar Sin, tare da wasu sassa 3 masu alaka da su, ta nuna yadda cikin shekarun baya bayan nan, yanayin rayuwar halittun ruwa ke kara kyautata a cikin Kogin Yangtze.
Sanarwar da sassan suka fitar a Litinin din nan, ta ce matakan da aka dauka, irin su dakatar da kamun kifi a kogin na Yangtze sun haifar da kyakkyawan sakamako mai nagarta.
A shekarar 2021 ne aka sanya takunkumin hana kamun kifi na shekaru 10 a wasu sassan kogin na Yangtze, da nufin farfado da yawan halittun ruwa dake rayuwa cikin kogin. (Saminu Alhassan)