Taron manyan hafsoshin tsaron kungiyar ECOWAS ya ce bai ji dadin yadda kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar ba su turo wakilai ba
2024-08-11 13:49:39 CMG Hausa
Manyan hafsohin tsaron kasashen dake cikin kungiyar Ecowas sun sha alwashin kare martabar demokradiyya tare da kyautata sha`anin zaman lafiyar yankin.
Sun tabbatar da hakan ne a karshen babban taron da suka gudanar karo na 42 a birnin Abuja ranar juma`a 9 ga wata.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi bagwai ya aiko mana da rahoto.
Babban hafsan tsaron Najeriya Janaral Christopher Musa shi ne ya karanta bayanin bayan taron, inda ya kara jaddada kudirin mahalartar taron wajen kare gwamnatin demokradiyya tare da yaki da ayyukan ta`addanci wanda yake barazana ga dorewar mulkin siyasa da kwanciyar hankali a shiyyar.
Janaral Christopher Musa wanda ya yaba mutuka bisa irin gudumowar da mahalarta taro suka bayar ta fuskar shawarwari da dabarun da za su samar da dauwamammen zaman lafiya da cigaban tattalin arziki a kasashe mambobin kungiyar, wannan kamar yadda ya ce alama ce dake nuna karuwar hadin kai dake tsakanin kasashen, ko da yake dai ya bayyana takaicin gaza zuwa wakilan kasashen nan uku wajen taron da aka shafe kwanaki uku ana gudanarwa wanda abun damuwa ne mutuka ga kungiyar ta Ecowas.
“Mun ji takaicin rashin zuwan takwarorin mu daga Nijar, mali da kuma Burkina Faso wajen wannan taro, za ku iya ganin wuraren zaman da aka ware masu dauke da tutocin kasashen su amma babu kowa, mun yi hakan ne domin mu shaidawa duniya cewa dukkannin su ba makiya ba ne, `yan uwa ne gare mu”
Ya ce babu kasa daya tilo da za ta iya shawo kan matsalolin dake damun shiyyar ita kadai ba tare da an hada karfi ba.(Garba Abdullahi Bagwai)