logo

HAUSA

Sabon jakadan Sin ya isa Najeriya domin kama aiki

2024-08-11 20:37:03 CMG Hausa

Sabon jakadan Sin a Najeriya kuma babban jakadan Sin a kungiyar ECOWAS Yu Dunhai, ya isa birnin Abuja babban birnin Najeriya a jiya Asabar domin kama aiki.

Yu Dunhai shi ne jakada na 15 na kasar Sin a Najeriya, kuma shi ne babban jakadan Sin na 7 a kungiyar raya kasashen yammacin Afirka ko ECOWAS.(Safiyah Ma)