logo

HAUSA

An gudanar da harkoki daban daban domin bikin Qixi na al’ummar Sinawa

2024-08-11 15:15:05 CMG Hausa

Mahukunta a sassan daban daban na kasar Sin, sun shirya harkoki daban daban domin bikin Qixi, wato bikin ranar masoya na al’ummar Sinawa wanda a bana ya gudana a jiya Asabar.

Cikin irin abubuwan da aka gudanar akwai kasuwar cin nau’o’in abinci da harkokin raya al’adu, da hadakar bikin aure na mutane da dama, da harkokin yawon bude ido masu kunshe da abubuwan musamman na al’adu, da dabi’un al’ummun sassan kasar Sin.

Mashirya harkokin sun ce burin gudanar da su shi ne cin gajiya daga albarkatun al’adu masu nasaba da bikin Qixi, da kara raya kyawawan akidu don inganta dankon zumuncin iyali da alakar masoya, da samar da sabon salon wayewar kai na zamantakewa. (Saminu Alhassan)