Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 94 a Nijar
2024-08-10 15:57:51 CMG Hausa
Hukumomin kasar Nijar sun ce, ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 94, yayin da wasu 93 suka jikkata, kuma bala’in ya shafi wasu 137,156 a jamhuriyar Nijar tun farawar damina a watan Mayu.
Ministar agajin jin kai da bala’u, Aissa Lawan Wandarma ce ta tabbatar da hakan a wani taron manema labarai da aka yi a ranar Alhamis, inda ta ce, daga cikin wadanda suka mutu, 44 sun mutu ne a sanadiyyar ambaliyar ruwa, yayin da wasu 50 suka mutu sakamakon rugujewar gidaje.
A cewar ministar, dukkanin yankuna takwas na kasar ne ambaliyar ruwa ta shafa, wadanda suka hada da kauyuka 692, da kananan hukumomi 129 da kuma larduna 46.
Har ya zuwa yau, ana ci gaba da gudanar da ayyukan rarraba abinci, tare da tarin kayayyayi da suka kunshi kayan abinci da wadanda ba na abinci ba dake kan hanya.
Bugu da kari, gwamnati ta dauki matakan da suka dace domin ganin duk mutanen da ambaliyar ta shafa sun samu tallafin da suke bukata. (Yahaya)