Jami'in MDD ya yaba da samar da fasahar Juncao don bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi a Afirka
2024-08-10 17:00:15 CMG Hausa
Jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya yabawa kokarin kasar Sin na koyar da fasahar noman Juncao ga al'ummomin kasashen Afirka, tare da bayyana karfinta na kawo sauyi a fannin tattalin arziki da samar da guraben ayyukan yi.
Earle Courtenay Rattray, darektan ofishin babban sakataren MDD ya bayyana ra'ayinsa a cikin hirar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya-bayan nan, a gefen taron horaswa game da fasahar Juncao da aka yi a gundumar Huye na kasar Rwanda, ga mahalarta na kasashen Afrika.
Rattray ya ce, manufar yin amfani da fasahar Juncao ta yi daidai da manufofin farko na MDD na inganta ci gaba mai dorewa. Ana amfani da fasahar ta Juncao, ta yadda wanda ke amfani da ita zai iya samunta cikin sauki a wurin, kuma a tunaninsa wannan ita ce ainihin fa’idarta.
Juncao, wani nau'in ciyawa ce kuma muhimmin albarkatun noma don noman leman kwado, wanda Lin Zhanxi na jami'ar aikin gona da gandun daji ta Fujian ta kasar Sin ya kirkira a shekarun 1980. Kuma kawo yanzu sama da kasashe 100 sun amfana da ita. (Yahaya)