Taron manyan hafsoshin tsaron kasashen dake kungiyar ECOWAS ya kawo shawarar karfafa alaka domin shawo kan barazanar tsaro a shiyyar
2024-08-10 16:29:26 CMG Hausa

Ministan tsaro a tarayyar Najeriya Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya bukaci kwamitin manyan hafsoshin tsaron kungiyar ECOWAS da ya karfafa alakar aiki tare domin shawo kan kalubalen tsaro da shiyyar ke fuskanta.
Ya bukaci hakan ne ranar larabar 7 ga wata a birnin Abuja a wajen bude babban taro karo na 42 na manyan hafsoshin tsaron mambobin kasashen kungiyar ECOWAS, taron wanda kuma aka kammala shi jiya Jumma’a 9 ga wata.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Taron wanda ya samu halartar manyan dakarun sojin kasashen, an shirya shi ne hususan domin tattauna matsalolin tsaro da kasashen yammacin Afrika ke fuskanta.
Ministan tsaron na Najeriya ya jaddada mahimmancin hada karfi wajen guda domin yaki da ayyukan ta’addanci da sauran laifuka da ake aikatawa a kan iyakoki.
Alhaji Badaru Abubakar ya ce taron da aka fara zai kuma kara mayar da hankali sosai kan shirin bayar da gudummawar tsaro a kasar Saliyo.
“Ya zama wajibi cewa sai lallai an hada karfi wurin guda tare da musayar kwarewa za a iya shawo kan wadannan matsaloli gaba dayan su.”
Shi ma da yake nasa jawabin babban hafsan tsaron Najeriya Janaral Christopher Musa, ya ce hakika irin wannan taro zai kasance babbar hanyar lalubo hanyoyin wanzar da zaman lafiya a nahiyar baki daya.
“Batun hada kai wajen aiki tare yana da mutukar muhimmancin gaske wajen gano musabbabin matsalolin tsaro da kuma dakile afkuwar sa a shiyyar mu.”(Garba Abdullahi Bagwai)
