logo

HAUSA

Yawan kudin cinikin samar da hidima na shigi da fici a farkon rabin bana a kasar Sin ya karu da 14%

2024-08-09 21:18:18 CMG Hausa

Bisa alkaluman da ma’aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin ta gabatar a yau, an ce, cinikin samar da hidima na kasar Sin ya samu bunkasuwa cikin sauri a farkon rabin shekarar bana, yawan kudin cinikin shigi da fici ya kai kudin Sin Yuan biliyan 3598.03, wanda ya karu da kashi 14 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara.

Alkaluman sun shaida cewa, yawan kudin cinikin daga samar da hidima na fici na kasar Sin a farkon rabin bana ya karu da kashi 10.7 cikin dari, kuma yawan kudin cinikin na shigi ya karu da kashi 16.4 cikin dari. Yawan gibin kudin cinikin ya kai Yuan biliyan 662.87.

An kiyaye samun bunkasuwar sha’anin samar da hidimar yawon shakatawa cikin sauri. A farkon rabin bana, yawan kudin sha’anin yawon shakatawa na shigi da fici na Sin ya kai Yuan biliyan 961.71, wanda ya karu da kashi 47.7 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara, sha’anin yawon shakatawa ya kasance a matsayin farko na cinikin samar da hidima a kasar Sin. (Zainab Zhang)