logo

HAUSA

Firaministan Fiji zai ziyarci kasar Sin

2024-08-09 21:30:32 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yau Juma’a cewa, bisa gayyatar da firaministan kasar Sin Li Qiang ya yi masa, firaministan kasar Fiji Sitiveni Rabuka zai kawo ziyara kasar Sin daga ranar 12 zuwa ta 21 ga watan Agusta.

Mao ta bayyana hakan ne lokacin da aka bukaci ta yi karin bayani da kuma fatan kasar Sin game da ziyarar. Inda ta ce, a yayin ziyarar, shugabannin kasashen biyu za su yi musaya mai zurfi kan dangantakar dake tsakanin Sin da Fiji, da kuma muhimman batutuwan da suka shafi muradun kasashen biyu.

Ta kara da cewa, kasar Sin ta karbi shugabannin kasashen tsibiran tekun Pasifik da dama a bana, kuma firaminista Sitiveni Rabuka shi ma wani shugaba na daban ne da zai ziyarci kasar Sin bisa gayyatar da aka yi masa, wanda hakan ke nuni da dangantakar kut da kut tsakanin Sin da yankin kudancin tekun Pasifik. (Yahaya)