An kyautata yanayi da ma’aunin ci gaban matsakaita da kananan kamfanonin kasar Sin na watan Yuli
2024-08-09 15:41:50 CMG Hausa
Bisa alkaluman da kungiyar kula da kamfanoni matsakaita da kanana na Sin ta fitar yau Jumma’a, ma’aunin ci gaban matsakaita da kananan kamfanonin kasar ya kai 88.9 a watan Yuli, wanda ya yi daidai da na watan Yuni, wato adadin bai ci gaba ko raguwa ba, wanda hakan ya nuna yanayin ci gaban matsakaita da kananan kamfanoni ya samu kyautatuwa.
Daga cikinsu, a watan Yuli, ma’aunin tattalin arziki daga manyan fannoni, da ma’aunin kasuwa, da kuma ma’aunin moriya sun sauya daga yanayin faduwa zuwa komawa, kana ma’aunin yin kasuwanci, da ma’aunin zuba jari sun sauya daga faduwa zuwa samun daidaito, yayin da ma’aunin yawan kudin da ake kashewa wajen sayen kayayyaki, da ma’aunin jarin da aka zuba, da kuma ma’aunin ’yan kwadagon da aka dauka sun yi ta raguwa.
Bugu da kari, a watan Yuli, ma’aunin masana’antun gine-gine, da gidaje, da ba da hidimomi, da kuma manhajar yada labarai sun karu sama da na watan da ya gabace shi, kuma ma’aunin masana’antu ya yi daidai da na watan da ya gabata, yayin da ma’aunin sufuri, da tallace-tallace, da matsuguni da abinci suka ragu.
Wani jami’in kungiyar kula da harkokin kamfanoni matsakaita da kanana na Sin ya bayyana cewa, alkaluman sun nuna farfadowar kwarin gwiwar samun ci gaba na kamfanoni, yayin da hasashen da aka yi wa kasuwa ya kara kyautatu. (Safiyah Ma)