logo

HAUSA

Sin ta ware yuan miliyan 649 domin ayyukan shawo kan ambaliyar ruwa da agajin jin kai

2024-08-08 11:02:40 CMG Hausa

Ma’aikatar kudi ta kasar Sin ta sanar da ware yuan miliyan 649, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 91, domin tallafawa ayyukan shawo kan ambaliyar ruwa, da samar da agajin jin kai a sassa daban daban na kasar.

Wata sanarwar da ma’aikatar ta fitar a jiya Laraba, ta ce gwamnatin tsakiya ta amince da fitar da kudaden a ranar Talata, kuma za a yi amfani da su musamman wajen shawo kan tasirin mahaukaciyar guguwa, da ambaliyar ruwa, da kuma ayyukan agajin jin kai a lardunan Liaoning, da Jilin, da Heilongjiang, da Anhui, da Fujian, da Shandong. Sauran sun hada da Henan, da Hubei, da Hunan, da Sichuan, da Shaanxi da Gansu, da jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai da kuma birnin Chongqing.

Kazalika, za a yi amfani da kudaden wajen taimakawa wadannan yankuna a fannin gyara ababen more rayuwa masu nasaba da adana ruwa, da gudanar da bincike da kawar da hadurra, ta yadda za a kai ga maido da ayyukan samar da ruwa masu inganci, da kyautata ababen more rayuwa da ake bukata a wannan gaba da ake fama da ambaliyar ruwa. (Saminu Alhassan)