Kasar Sin tana da likitocin kauyuka miliyan 1.1
2024-08-08 20:11:14 CMG Hausa
Alkaluman da aka fitar a baya-bayan nan sun nuna cewa, kasar Sin na da ma’aikatan kiwon lafiya miliyan 4.95, wadanda suka hada da likitoci miliyan 1.1 dake aiki a yankunan karkara.
Sanarwar da hukumar lafiya ta kasar Sin wato NHC ta fitar a yau Alhamis ta bayyana cewa, suna ba da gudummawa ga gagarumin aikin rigakafin cututtuka da ayyukan jinya tsakanin al’umma a kasar.
A halin yanzu, akwai cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 980,000 a kasar Sin, wadanda ke kula da kusan kashi 52 cikin 100 na yawan ayyukan kula da lafiya da kasar ke yi, a cewar sanarwar NHC.
Sanarwar ta kara da cewa, bisa tushen shirye-shiryen gwaji don gina irin wannan kawancen lafiya a matakin gundumomi, za a kaddamar da wani tsari a duk fadin kasar da zai shafi dukkanin gundumomi kafin karshen shekarar 2027. (Yahaya)