Wakiliyar musamman ta Xi za ta halarci bikin rufe gasar wasannin Olympics ta Paris kuma za ta ziyarci Serbia
2024-08-08 19:58:46 CMG Hausa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta sanar a yau Alhamis cewa, wakiliyar musamman ta shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mambar majalisar gudanarwar kasar Sin Shen Yiqin za ta halarci bikin rufe gasar wasannin Olympics ta karo na 33 da za a yi a birnin Paris da sauran harkoki masu ruwa da tsaki daga ranar 9 zuwa ta 11 ga watan Agusta.
Mao ta kara da cewa, bisa gayyatar da gwamnatin kasar Serbia ta yi mata, Shen Yiqin za ta kuma ziyarci kasar ta Serbia daga ranar 12 zuwa ta 14 ga watan Agusta.
Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng ya halarci bikin bude gasar, yayin da ‘yar majalisar gudanarwar kasar madam Shen Yiqin za ta halarci bikin rufe gasar, dukkansu a matsayin wakilan shugaba Xi na musamman.
"Wannan ya nuna yadda kasar Sin take matukar mutunta da kuma goyon bayan ayyukan Olympics na kasa da kasa da ma aikin kasar Faransa a matsayin mai karbar bakuncin gasar. Kasar Sin ta yaba da nasarar da aka samu a gasar wasannin Olympics ta Paris ta shekarar 2024, tare da yi mata fatan cikakken nasara cikin kwanaki masu zuwa. (Yahaya)