logo

HAUSA

Shugaban Tunisia ya sallami firaministan kasar

2024-08-08 10:53:59 CMG Hausa

Shugaban kasar Tunisia Kais Saied, ya sallami firaministan kasar Ahmed Hachani a jiya Laraba.

Wata sanarwar da ofishin shugaban kasar ya fitar ce ta sanar da hakan tare da nadin ministan kula da harkokin al’umma Kamel Maddouri, a matsayin sabon firaminista ba tare da bayyana dalilin korar ba. 

A watan Agustan bara ne aka nada Ahmed Hachani a matsayin firaministan Tunisia. (Fa’iza Mustapha)