logo

HAUSA

Shugaban Zanzibar Ta Tanzania: Ba Za Iya Raba Ci Gaban Afirka Da Sin Ba

2024-08-08 11:21:26 CMG Hausa

Shugaban Zanzibar na Tanzania, Hussein Ali Mwinyi, ya halarci taron sa hannu kan yarjejeniyar ayyukan samar da lantarki ta PV da sauransu, wanda kamfanonin Sin suka zuba jari da kuma gina su a jiya Laraba.

Yayin da yake amsa tambayoyin dan jarida na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, mista Mwinyi ya bayyana cewa, dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, dandalin hadin gwiwa ne mai muhimmanci na cimma matsaya guda kan ci gaba, don haka yana da kyakkyawan fata sosai ga taron FOCAC na shekarar 2024 da zai gudana ba da jimawa ba. Kaza lika, zai koyi darussan Sin a fannin kawar da kangin talauci don kawo alheri ga al’ummar kasar.

Mwinyi ya kara da cewa, ta hanyar FOCAC, ana fatan Tanzania za ta jawo jari da yawa. A sa’i daya kuma, ya jinjinawa goyon baya da Sin ke baiwa Tanzania. Ya ce ba za a iya raba ci gaban Afirka da Sin ba, kasancewar Sin ta taka muhimmiyar rawa ga ci gaban Afirka. Ta kuma samu gagarumin ci gaba a fannonin samar da manyan ababen more rayuwa, da aikin noma, da raya fannin yawon shakatawa da sauransu.

Ban da hakan, Sin ta cimma wata babbar nasara a fannin kawar da kangin talauci. Yana fatan koyon darussan Sin, ta yadda zai aiwatar da matakan tsame al’ummarsa daga kangin fatara. (Safiyah Ma)