logo

HAUSA

Nan da mako guda za a aiwatar da shirin shigo da kayan abinci ba tare da biyan haraji ba a Najeriya

2024-08-08 09:30:54 CMG Hausa

Shugaban hukumar Kwastam ta tarayyar Najeriya Mr Bashir Adeniyi ya tabbatar da cewa, cikin mako guda hukumar za ta fara aiwatar da shirin kin karbar haraji na wasu kebantattun kayan abinci da gwamnati ta amince a shigo da su kasar.

Ya tabbatar da hakan ne da yammacin Talata 6 ga wata a birnin Abuja yayin wani taron manema labarai.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Shugaban hukumar ta kwastam ya sanar da cewa, fara aiki da umarnin gwamnatin dai ya biyo bayan kammala dukkannin tsare-tsaren da suka kamata daga ma’aikatar kudi ta tarayya domin dai samun nasarar aikin.

Ya ce, jinkirin fara shigo da kayan abincin yana da nasaba da kokarin ganin an daidaita al’amura tare kuma da kare bukatun manoman kasar ta yadda sana’ar su ba za ta samu koma baya ba da kuma karyar da farashin kayan abinci a cikin gida.

Mr Basher Adeniyi ya tunatar da ’yan Najeriya cewa, akwai bukatar a lura sosai wajen cin gajiyar shirin ta hanyar bin sharadai da ma’aikatar kudi ta gindaya.

Ya tabbatar da cewa cikin mako guda wadannan sharudai za su fito kuma hukumar za ta bayyanawa al’umma, kuma dage takunkumin shigo da kayan abincin na wucin gadi ne domin dai kawai saukakawa al’umma matsalar tsadar abinci.

Alkama da Masara da Shinkafa na daga cikin kayan da aka amince a shigo da su ba tare da biyan kudin haraji ba ga gwamnati. (Garba Abdullahi Bagwai)