Kasar Burkina Faso tana shirin gina wata tashar samar da makamashin nukiliya
2024-08-08 10:26:07 CMG Hausa
Mu je a jamhuriyyar Burkina Faso inda, ministan da ke kula da makamashi, Yacouba Zabre Gouda ya gana da wata tawagar kwararru na kamfanin kasar Rasha Rosatom daga ranar 6 zuwa 7 ga watan Augustan shekarar 2024 a birnin Ouagadougou.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Bangarorin biyun sun tattauna kan shirin gina wata tashar samar da makamashin nukiliya a kasar Burkina Faso.
Tun yau da ’yan watanni, kasar Burkina Faso ta dukufa cikin nazarin wani shirin gina wata tashar samar da makamashin nukiliya.
A cewar ministan makamashi, Yacouba Zabre Gouda, kasarsa na son ta hanyar nukiliya warware matsalolinta baki daya na karancin makamashi ko wutar lantarki.
A cewar minista Gouda, wannan ziyara na janyo fatan alheri bisa ga damammakin da wannan kamfanin kasar Rasha zai samar musamman ma hanyoyin magance makamashi a kasar Burkina Faso.
A karshe, ministan makamashin Burkina Faso, ya bayyana cewa, alkawari ne da shugaban kasar Burkina Faso Ibrahim Traore ya dauka domin kawo wa al’ummar kasarsa sauki wajen samun wadatanccen makamashi mai tsafta.
Mamane Ada, sashen Hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.